HausaTsohon Tarihi

WAYEWAR KAN MUTANEN INDIA

Wayewar Kan Mutanen India wato Indian Civilization ita ma tana cikin na farko a cikin wayewar kai da mutane suka fara samu a duniya.

Ita Wayewar Kan Mutanen India ta fara ne a Kwarin Indus dake tsakanin jerin duwatsun Himalaya da na Hindu Kush a arewa, da kuma duwatsun Sulaiman daga yamma. Kuma wannan Wayewar ta mutanen India ta bunkasa ne a tsakanin shekaru 3300 zuwa 1900 kafin al-Masihu.

Kamar sauran wayewar kan mutane da aka samu a duniya, Wayewar Kan Mutane ta India ta bunkasa ne a cikin biranen Harappa da kuma biranen Mahenjo-Daro, da kuma wasu manyan garuruwa 70 wadanda suka bunkasa ta hanyar noma.

Kwarin Kogon Indus, ya kasance yana tunkudo ruwa tare da kasar laka mai kyau zuwa yankunan Harappa da Mahenjo-Daro, wanda ya bawa mutane damar yin noma. A bisa bincike na masana archaeology da suka gudanar, ya nuna cewa biranen Harappa da Mahenjo-Daro sun kasance kusa da Kogin Ravi wanda shi kuma wani bangare ne na hannuwan Kogin Kwarin Indus. Haka kuma bincike ya nuna cewa wadannan birane na Harappa da Mahenjo-Daro sun kasance tsararrun birane wadanda aka zagaye su da manyan dogayan ganuwa.

Kuma a bangaren tattalin arziki, masana archaeology sun hako irin kayan kere kere na yankin Harappa a biranen Mesopotamia. Wanda hakan take nuna cewa biranen yankin India sun yi hulda ta kasuwanci da biranen yankin Mesopotamia.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button