TARIHIN TSOHUWAR DAULAR GIRKAWA

A History and Culture Hub

TARIHIN TSOHUWAR DAULAR GIRKAWA

Taswirar Daular Girkawa. Author : Megtias. Source : creativecommons.org

Tsohuwar Daular Girkawa wadda a turance ake kira da Ancient Greece, wata wayewar kan mutane ce ta al’ummar kabilun Girkawa (Greeks) wadda ta samu gindin zama a birane da daban-daban masu zaman kan su da ake kira ‘Acropolis’ a yankin Tsibirin Kogin Agayen (Aegean Sea), tsakanin shekara ta 1200 kafin al-Masihu zuwa wajejen shekara ta 600 Miladiyya.

Wannan lokaci na Tsohuwar Daular Girkawa zamani ne da kabilun Girkawa suka samar da tsarin siyasa, zamatakewa, da kuma harkar ilmi a biranen na Girkawa daban-daban. Ko da yake wadannan birane sun kasance masu ikon kan su (independents), amma kuma duk suna daukan kan su a matsayin al’umma daya, sakamakon duk yare guda suke yi.

Masana tarihi da yawa sun bayyana zamanin Tsohuwar Greece a matsayin zamanin da aka kafa tushen ilmin boko na yammacin duniya akan siyasa (political science), falsafa (philosophy), da kuma kimiyya da fasaha ( science and technology ). Domin kuwa a zamanin Girkawa, musamman a birnin Athens, masana ilmi a fannoni da yawa sukan taru domin su tattauna akan abubuwan ilmi daban-daban. Irin wadannan manyan masana sun hada da Socrates, Plato, Aristotle, da kuma Aristophanes.

KAFUWAR YANKUNAN GIRKAWA

Tarihi ya tabbatar da cewa Yankunan biranen Girkawa sun fara ne lokacin da kabilun na Girkawa suka yiwo kaura daga arewa zuwa Tsibirin Kogin Aegean, wanda kabilun Mycenaean suke rayuwa. Saboda haka Girkawa suka mamaye wadannan kabilu na Mycenaea, kuma suka rarrabu suka kafa birane daban-daban.

MANYAN BIRANEN GIRKAWA NA ATHENS DA SPARTA

ATHENS

Birnin Athens ya kasance daya daga cikin biranen Greece masu ikon kan su, kuma daya daga cikin manya masu tasiri a tarihin Girkawa. Domin kuwa, tarihi ya tabbatar da cewa a birnin Athens ne aka yankewa ilmin boko na yammacin duniya (Western Education) cibiya.

Birni mai ikon kan sa na Athens ya zama cikakken birni ne, bayan da wani shugaba mai suna Pisistratus ya samu mulkin birnin a shekarar 560 kafin al-Masihu. Kuma Shugaba Pisistratus ya kawo gyare-gyare kamar bada kasar noma ga yan Asalin Athens wanda ba su da ita. Sannan kuma ya taimaka wajen bunkasar al’adu ta hanyar bada gudunmawa ga masu zane da kuma mawaka.

Dimokaradiyya (Democracy) a Athens

Birnin Athens ya kasance birni na farko da ya samar da kuma fara gudanar da tsarin dimokaradiyya a tarihin duniya. Wannan kuwa ya tabbata nne lokacin da Cleisthenes ya zama shugaban birnin Athens a shekara ta 506 kafin al-Masihu. Lokacin da ya zama jagoran birnin na Athens, sai ya bawa yan mutanen Athens damar su fara zabar wakilan su don gudanar da shugabanci. Don haka ne ma Athens ta zama birni mafi daukaka akan sauran biranen da suke a fadin Daular Girkawa.

A tsarin dimokaradiyyar birnin Athens, yan asalin birnin wanda suka cika shekara 18 akan basu damar zabar wakilai ko kuma su tsaya a zabe su. Bayan jama’a sun zabi wakilan su guda 500, damar yin doka da shugabanci tana komawa ne ga wadannan wakilai da suka zaba wanda suke kafa Majalisar Mulkin Birnin Athens.

Ilimi a Birnin Athens

Birnin Athens ya samu shaharar sa ne da kuma tasiri, sakamakon kasantuwar sa cibiyar ilmi ta Girkawa. Domin kuwa, masana tarihi sun tabbatar da cewa ilimi da fasahar boko ta Yammacin Duniya ta samo asali ne daga ci gaban ilmin birnin Athens.

Athens ta bunkasa a bangaren ilmi ne, zamanin shugaba Pericles wanda ya karfafawa masana ilmi a birnin Athens gwiwa akan al’amura da suka shafi tunani da kuma hujja wato a turance ‘philosophical thinking’ ko ‘reasoning’. Don haka ne ma birnin Athens ya samar da manya-manyan malaman falsafar nan (philosophers) da ilimin boko a duniya yake ji da su. Wadannan Malamai kuwa sun hada da Socrates, Plato, Aristotle, Aristophanes, da sauran su.

SPARTA

Birnin Sparta kuma ya zama muhimmin birnin Girkawa sakamakon karfin mayaka. Domin kuwa Sparta ya kasance birni ne mai alfahari da karfin soja, wanda har ya kasance suna iya bawa sauran biranen Girkawa tsaro. Saboda haka ne ma birnin Sparta ya kasance ba a zagaye da ganuwa ba. Har suna da wani kirari da yake cewa “Katangar karfin soja, tafi katangar kasa”.

Tsarin Soja a Sparta

Kamar yadda muka fada, birnin Sparta ya samu shaharar sa ne saboda karfin mayaka da yake da shi.

Sojojin Sparta sun sami horo na dabaru da juriya a fagen yaki. Kamar yadda yake a Tsarin Mulkin birnin Sparta da ake kira ‘Lyucurgan’, ya nuna cewa duk yaron da ya cika shekara 7, to dole ne ya shiga makarantar koyon yaki, kuma ya kasance ya shiga soja idan ya cika shekara 18, sannan yayi ritaya idan ya cika shekara 60.

Shine ma yasa a tarihi nasarar mayakan Sparta a yaki ta rinjayi rashin ta.

Tsarin Gwamnati a Sparta

Mutanen Sparta kamar na birnin Athens, sun samar da tsarin shugabanci irin na dimokaradiyya.

A tsarin, duk wani mutum da ya kai shekara 30 yana da yancin zaba ko shiga a dama da shi a cikin Gwamnati. Saboda haka mutanen birnin Sparta suna zabar mutane daga cikin su wanda za su kafa majalisun mulki guda 2 kamar haka :

  1. Majalisar Manya: Wannan Majalisa ta kun shi wakilai ne wadanda suka kai shekara 60, wato ‘senior citizens’ a turance. Kuma ana zabar su ne domin suyi doka da kuma tsawatarwa a cikin al’umma.
  2. Majalisar Yan Biyar : Wannan Majalisa ita kuma ta kun shi mutum 5 ne wadanda ake kira da ‘Ephors’ a yaren Girkawa. Su kuma Majalisar Manya ce take zabo su, domin su zartar da dokokin da suka samar.


ADDININ GIRKAWA

Addinin da ake yi a duk fadin biranen Tsohuwar Daular Girkawa ya kasance na bautawa alloli da yawa. Shugaban allolin kuwa shine Zeus, wanda Girkawa suke ba shi matsayin Sarkin allolin Greece.

Haka kuma ko wane birnin Girkawa yana da ubangijin da suka rike a matsayin wakilin su a wajen Shugaban alloli wato Zeus. A misali, mutanen Sparta sun rike Ares (ubangijin yaki ) a matsayin majibincin lamarin su. Mutanen Athens kuma, sun rike karamar ubangijiya mai suna Athena (ubangijiyar basira) a matsayin majibinciyar lamarin su.

KARKAREWA

Idan mu kayi la’akari da bayanan da suka gabata, zamu ga cewa Tsohuwar Daular Girkawa ta kasance ci gaba na farko-farko da dan adam ya fara samu a tarihin duniya.

Haka kuma zamu ga cewa a zamanin Tsohuwar Daular Girkawa ta Greece ne, aka kafa tubalin ilimin boko na Yammacin duniya wato a turance ‘Western Education’.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.