HausaMasarautar Kano

TARIHIN MULKIN FULANI A MASARAUTAR KANO

 

 

Tambarin Masarautar Kano. Source : Kano Emirate Council

 

Tarihin Mulkin Fulani a Masarautar Kano ya samo asali ne daga faruwar Jihadin Shehu Usman Danfodio, wanda ya tabbata a shekarar 1804.

Tarihin Mulkin Fulani a Masarautar Kano ya samo asaline tun bayan Jihadin Fulani na Shehu Danfodio wanda ya kasance wani juyin juya hali da aka gudanar a fadin kasar Hausa da kuma wasu sassa na Arewacin Nigeria ta yanzu. Wanda yayi sanadiyyar kawar da mulkin sarakuna Hausawa a Kasar Hausa, kuma aka maye gurbin su da Sarakunan Fulani, wanda suka kafa mulki mai tafiya da Shari’ar Musulunci karkashin Daular Fulani mai hedikwatar mulki a Sokoto.

Kafin kafuwar Mulkin Fulani a Masarautar Kano, tarihi ya tabbatar cewa addinin Musulunci yazo kasar Hausa ne ta hanyar malamai masu yawon wa’azi daga kasar Mali a wajejen Karni na sha hudu ( wato 14th century). A misali, a Kano Sarkin Kano Yaji Dan Tsamiya wanda yayi mulki daga 1349 zuwa 1385 ne ya fara karbar addinin Musulunci a tarihin Kano. Haka kuma sauran sarakunan Kasar Hausa suka karba a masarautu kamar Katsina, Daura, Gobir, Zazzau, da sauran su.

To amma bayan wani zamani, sai Sarakunan Kasar Hausa suka karkace daga koyarwar Addinin Musulunci zuwa tsafe-tsafe da harka da bokaye. Haka kuma yake-yake da kamen bayi da kuma zalunci ga talakawa suka zama ruwan dare. To ana cikin wannan hali ne, cikin farkon Karni na sha tara, wato wajejen Shekara ta 1804, sai wani Malamin Addinin Musulunci mai Suna Shehu Usman Danfodio ya bayyana a Kasar Gobir, yana wa’azi yana kira ga Sarakunan Kasar Hausa da kuma sauran al’ummar Hausawa da Fulani da su daina hada Bautar ALLAH (SWA) da wasu ayyuka na shirka. Haka kuma ya yi kira ga Sarakunan Kasar Hausa da su zama masu adalci. To amma, wannan wa’azi na Shehu Danfodio bai yi wa Sarakunan Kasar Hausa dadi ba, musamman Sarakunan Kasar Gobir. Wannan ta janyo Sarakunan Kasar Gobir kamar su Bawa Jangwarzo, Yakubu, Nafata, da kuma Yumfa da suka yi sarautar Gobir duk suka dinga tsangwamar Shehu Danfodio, har ta kai Shehu Danfodio ya yi Hijra daga garin sa na haihuwa wato Degel zuwa wani gari da ake kira Gudu. To daga nan ne Sarkin Gobir Yumfa ya ayyana yaki tsakanin sa da Shehu Usman Danfodio. To amma sai ALLAH YA bawa Shehu Danfodio nasara akan Sarkin Gobir Yumfa, a wani yaki da ake cewa da shi “Yakin Tabkin Kwatto”.

Wannan nasara ta Shehu Usman Danfodio akan Sarkin Gobir Yumfa, ita ce ta kawo karshen mulkin Masarautar Gobir. Saboda haka labarin wannan nasara ta zagaya a duk fadin Kasar Hausa dama sauran sassan Arewacin Nigeria ta yanzu. Don haka ne ma sauran Fulani dake fadin Kasar Hausa da sauran sassan Arewacin Nigeria ta yanzu suka dinga tuttudowa zuwa gurin Shehu Danfodio domin ya ba su tuta don su kaddamar da jihadi a masarautun su. Manyan mutanen da Shehu Usman Danfodio ya bawa tutar Jihadi sun hada da :

 1. Malam Sulaimanu — Kano
 2. Malam Umaru Dallaji — Katsina
 3. Malam Musa — Zazzau (Zaria)
 4. Malam Isyaku — Daura
 5. Malam Malam Yakubu — Bauchi
 6. Malam Buba Yero — Gombe
 7. Malam Modibbo Adama — Adamawa
 8. Malam Sambo — Hadejia
 9. Malam Ibrahim Zaki — Katagum
 10. Malam Gwani Mukhtar — Misau
 11. Malam Dendu — Nupe (Bida)
 12. Malam Alimi — Ilorin

Wadannan jerin manyan Fulani, sune wanda Shehu Usman Danfodio ya bawa Tutar Jihadi, kuma suka kaddamar da ita a yankunan su.

Taswirar Daular Fulani ta Sokoto

SARAKUNAN FULANI A KANO 1807 – 2014

Kamar yadda muka fada, bayan samun nasarar Jihadi da Shehu Usman Danfodio ya yi a yankin sa na Gobir, sai kuma sauran yankunan Kasar Hausa suka kaddamar da nasu Jihadin.

Tarihi ya tabbatar da cewa a Kano ma jagorin Fulani sun kaddamar da Jihadi a 1804 kuma suka sami nasarar kammala shi a 1807 bayan da suka tunbuke Sarkin Kano na wannan lokacin wato Sarki Muhammadu Alwali wanda hakan ne kuma Wadannan jagorori sun hada da :

 1. Malam Muhammadu Danzabuwa —daga Kabilar Fulani Danejawa
 2. Malam Muhammadu Gabuwa — daga Kabilar Fulani Mundubawa
 3. Malam Jamo — daga Kabilar Fulani Sullubawa
 4. Malam Jibir — daga Kabilar Fulani Yolawa
 5. Malam Bakatsine — daga Kabilar Fulani Jobawa
 6. Malam Inusa Dabon Dambazau — daga Kabilar Fulani Dambazawa

Saboda haka ne bayan nasarar Jihadin Kano, sai wadannan shugabannin Fulani na Kano suka tafi Sokoto gurin Shehu Usman Danfodio don ya zabi sarki a cikin su. Kamar yadda Wazirin Kano Abubakar Dokaji ya bayyana a littafin sa “Kano Ta Dabo Ci Gari” yace bayan da suka isa, sai Shehu yace “waye limamin ku” sai suka ce “dalibin ka ne Sulaimanu”, to ance sai Shehu Danfodio ya yi amfani da kalmar Musuluncin nan ta ” Imamukum Amirukum“. Don haka aka ce da wannan Shehu Usman Danfodio ya dogara wajen nada Malam Sulaimanu dan Abahama na Kabilar Fulani Mundubawa a matsayin sabon Sarkin Kano na bayan Jihadi. Kuma tun daga lokacin zuwa yanzu anyi sarkunan Kano guda 14.

SARKIN KANO SULAIMANU (1807-1819)

Sarkin Kano Malam Sulaimanu dan Abahama ya fito ne daga Kabilar Fulani Mundubawa, kuma ya kasance daya daga cikin almajiran Shehu Usman Danfodio na Kano. Sarki Sulaimanu ya kasance sarki na farko a Tarihin Mulkin Fulani a Masarautar Kano.

Sarki Sulaimanu ya kasance zabin ALLAH wanda duk mutanen Kano basu taba kawo wa a ran su cewa zai zama Sarkin Kano na bayan Jihadi ba. Saboda, shi Malam Sulaimanu baya cikin Manyan jagororin Fulani a Kano, sannan kuma lokacin da aka tafi Sokoto gurin Shehu domin ya nada sabon Sarkin Kano, Malam Sulaimanu din dai baya nan. To amma kasancewar sa Limamin masu yin Jihadin Kano, sai Shehu ya nada shi Sarkin Kano.

Amma tarihi ya nuna cewa Sarkin Kano Sulaimanu ya hadu da kalubale na adawa daga wadannan shugabannin Fulani na Kano, wanda har sai da Shehu Usman Danfodio ya yi musu sulhu sannan ya samu nutsuwa a mulkin sa.

Bayan anyi sulhu, sai Sarkin Kano Sulaimanu ya kafa Majalisar Shari’a a fadar sa, wadda ta kunshi shugabannin Kabilun Fulani na Kano kamar haka :

 1. Malam Jamo — Sullubawa
 2. Malam Abdurrahman Goshi — Yolawa
 3. Malam Bakatsine — Jobawa
 4. Malam Inusa Dabon Dambazau — Dambazawa
 5. Malam Sani dan Malam Danzabuwa — Danejawa
 6. Malam Sani kanin Sarki Sulaimanu — Mundubawa
 7. Malam Yusufu Magajin Malam na Hausawa
 8. Malam Usman na Hausawa

Da wannan kafa Majalisar Shari’a ne, Sarkin Kano Sulaimanu ya fara cikakken mulkin Kanawa.

Masana tarihin Kano, sun bayyana Sarkin Kano Sulaimanu a matsayin mutum mai tsoron ALLAH, kuma mai kankan da kai. Har ance baya zama akan karagar mulki har sai idan zai yi hukunci. Sannan kuma bayan zaman fada ya kan fita zuwa wajen sana’ar sa, wato rafi domin yayi bulo na siyarwa.

Sarkin Kano Malam Sulaimanu dan Abahama ya rasu a cikin shekara ta 1819 Miladiyya bayan ya kwashe shekaru 12 yana sarauta.

SARKIN KANO IBRAHIM DABO (1819 – 1846)

Sarkin Kano Ibrahim Dabo dan Malam Mamuda ya zama Sarkin Kano na biyu a Tarihin Mulkin Fulani a Masarautar Kano Sarakuna Fulani ne bayan rasuwar Sarki Sulaimanu a shekarar 1819. Tarihi ya nuna cewa Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ne ya aiko da wasika yana umartar Jagororin Fulanin Kano da su zauna su shawarta akan yana so ya nada Malam Ibrahim Dabo kanin Malam Jamo na Kabilar Fulani Sullubawa a matsayin Sarkin Kano, to amma su shawarta akan ko ya dace da ya zama Sarkin Kanon. To ance sai wadannan Shugabannin Fulani karkashin jagorancin Malam Jibir na Kabilar Fulani Yolawa suka tattauna kuma suka girmama Sarkin Musulmi Bello ta hanyar yin mubayi’a ga zabin da yayi na Malam Ibrahim Dabo kanin Malam Jamo na Kabilar Sullubawa. Sai dai an ce wasu yan tsirarin mutane sun ki yarda da zabin. Masana tarihin Kano sun ce Majalisar zaben Sarkin Kano ma ta samo asali ne daga wannan zama da aka yi. Shugabannin wannan zama kuwa sun fito ne daga Manyan Kabilun Fulani kamar haka :

 1. Yolawa — wanda daga bisani Sarkin Kano Dabo ya basu sarautar Madaki, kuma suke shugabantar zaman zabar Sarkin Kano har zuwa yau.
 2. Jobawa — aka basu sarautar Makama wadda suke rike da ita har zuwa yau
 3. Sullubawa — sarautar Sarkin Dawaki Mai Tuta
 4. Dambazawa — sarautar Sarkin Bai

 

Tawayen Dantunku a zamanin Sarkin Kano Dabo

Tarihi ya nuna cewa Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo ya yi fama da matsalar tawaye a farkon mulkin sa, har ta kai yayi yaki mai yawa da yan tawaye.

Babban tawayen da Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo ya hadu da shi, shine na Sarkin Fulanin Arewacin Kano wato Malam Usman Dantunku na Kabilar Fulani Yarimawa. Ance, shi Malam Usman Dantunku ya kasance shugaban tara haraji na Sarkin Kano a fadin Arewacin Kasar Kano, sannan kuma a wani kaulin na tarihi ance lokacin da Jihadin Shehu Usman Danfodio ya fara, shima Malam Dantunku an bashi tutar Jihadi. Saboda haka ne, bayan Sarki Sulaimanu ya rasu Malam Usman Dantunku yaga cewar to shima fa lokacin sa yayi na cin gashin Kan sa, don haka ne ma sai yaki yiwa Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo mubayi’a.

Masana tarihin Kano, sun ce wannan dalili ne ma ya saka Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo ya kaddamar da yaki akan Malam Usman Dantunku. Ance an kwashe kimanin kusan shekaru 3 ana gwabzawa tsakanin dakarun Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo da na Sarkin Fulanin Arewacin Kano wato Malam Usman Dantunku. Har wani bature mai yawon neman sanin kasashe dan kasar Ingila wato Hugh Clapperton yaga yadda Malam Usman Dantunku yayi wa mayakan Sarkin Kano Dabo barna. Amma daga bisani Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo ya samu nasarar fatattakar Malam Usman Dantunku da mutanen sa har zuwa iyaka da Kasar Katsina. Da haka ne Sarkin Kano Dobo ya murkushe barazanar tawayen Dantunku da kuma sauran tawaye.

 

Kasaitar Sarkin Kano Ibrahim Dabo

Masana da Marubutan tarihin Kano, sun bayyana Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo a matsayin Kasaitaccen Sarki, wanda ya gyra sarautar Kano, kuma yayi tasiri a ciki ta hanyar samarwa tare da jaddada wasu al’adu na kasaita wadanda Kano ce kawai ta kebanta da su. Wadannan al’adu sun hada da :

 • Rike Tagwayen Masu
 • Zama akan karaga, sauran hakimai kuma suna zaune a kasa.
 • Yin nada mai kunne biyu
 • Saka Takalmi mai Gashin Jimina
 • Samar da Sarautun bayi masu kula da doka da oda kamar su Shamaki, Danrimi, Sallama, Sarkin Dogara, Kasheka, Turakin Soro, Sarkin Hatsi, Kilishi, da sauran su.
 • Banbanta yayan Sarki da na bayi, ta hanyar yi wa yayan bayi tsaga uku-uku a kunchin su.

Rasuwar Sarkin Kano Ibrahim Dabo

Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo ya rasu a shekarar 1846, bayan ya kwashe shekaru 27 yana Sarauta.

 

SARKIN KANO USMAN MAJE-RINGIM (1846-1855)

Sarkin Kano Usman I, wanda ake yi wa lakabi da Maje-Ringim shine babban dan Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo. Ya zama Sarkin Kano na uku Tarihin Mulkin Fulani a Masarautar Kano a shekarar 1846, bayan rasuwar mahaifin sa, wato Sarki Ibrahim Dabo.

A bisa Tarihin Mulkin Fulani a Masarautar Kano, ance shi Sarkin Kano Usman Maje-Ringim mutum ne mai tausayi da kuma sanyi wajen gudanar da mulki, wannan ce ma ta saka baya iya yin cikakken hukunci sai dai dan uwan sa Galadiman Kano Abdullahi ya zartar.

Sarkin Kano Usman Maje-Ringim ya rasu ne a Ringim, akan hanyar sa ta zuwa Hadejia don ya yaki Sarkin Hadejia Buhari, wanda Sarkin Musulmi ya umarta da a yaka saboda yayi wa Daular Usmaniyya tawaye. Ance rasuwar Sarkin Kano Usman a Ringim ne ya saka ake kiran sa da “Maje-Ringim”.

 

SARKIN KANO ABDULLAHI MAJE-KAROFI (1855 – 1882)

Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi dan Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo ya zama Sarkin Kano na hudu a Tarihin Mulkin Fulani a Masarautar Kano bayan rasuwar wansa, wato Sarki Usman Maje-Ringim a shekarar 1855.

Masana tarihin Kano sun bayyana Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi a matsayin mutum mai kwarjini da jarumtaka irin ta mahaifin sa Sarkin Kano Ibrahim Dabo. An ce shaharar sa ce ma ta saka ake yi wa duk wani Abdullahi lakabi da “Maikano”. An ce a zamanin sa ne aka fara bugawa Sarki bindiga idan zai fito ko zai shiga gida. Shine kuma ya gina Gidan Sarki na Nassarawa.

Haka nan a bangaren yaki, masana Tarihi sun ce shi Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi mutum ne wanda baya tsoron yaki, kuma ALLAH YA hore masa dabarun yaki. Wannan ce ma ta saka nasarorin sa a yaki suka rinjayi rashin su. A misali tarihi ya bayyana cewar mayakan Sarkin Ningi sun sha wahala a yakin da suka yi da Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi.

Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi ya rasu a cikin shekarar 1882 a Karofi ta Kasar Katsina akan hanyar sa ta zuwa Sokoto. Don haka ne ma rasuwar sa a Karofin, ta saka ake masa lakabi da “Maje-Karofi”.

 

SARKIN KANO BELLO (1882 – 1893)

Sarkin Kano Bello shima dan Sarkin Kano Ibrahim Dabo ne, ya kuma zama Sarkin Kano na biyar a jerin sarakuna a Tarihin Mulkin Fulani a Masarautar Kano a shekarar 1882, bayan rasuwar wansa, wato Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi.

Ance shi Sarkin Kano Bello ya kasance mutum ne mai yawan ilmin Addinin Musulunci da kuma yawan rokon ALLAH. Har ance baya yin bacci sosai da daddare, sai dai yayi ta rokon ALLAH akan ya bashi nasara a mulkin sa. Kuma shi Sarkin Kano Bello ance baya fita yaki, sai dai ya wakilta babban dan sa wato Galadiman Kano Tukur domin ya jagoranci rundunar mayakan Kano.

Sarkin Kano Bello ya rasu ne a shekarar 1893, bayan ya kwashe shekaru 11 yana Sarauta.

 

SARKIN KANO TUKUR (1893 – 1893 yan watanni kawai ya yi)

Sarkin Kano Tukur dan Sarkin Kano Bello dan Sarkin Kano Ibrahim Dabo ya zama Sarkin Kano na shida a jerin Sarakuna a Tarihin Mulkin Fulani a Masarautar Kano a shekarar 1893.

Ance bayan da Sarkin Kano Bello ya rasu duk Kanawa sun dauka cewar za’a nada Yusufu dan Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi ne a matsayin Sarkin Kano. To amma labarin sai ya zama na daban, domin Sarkin Musulmi Abdurrahman Danyen-Kasko yafi son Tukur dan Sarkin Kano Bello don haka ya yi umarnin da a nada shi a matsayin Sarkin Kano. To wannan dalili ne ya janyo barkewar Rigimar Basasar Kano wato a turance “Kano Civil War”.

Tarihi ya bayyana cewa, Galadiman Kano Yusufu ya jagoranci rundunar mayaka wadda ta kawo karshen mulkin Sarkin Kano Tukur. To amma kafin karewar gwagwarmayar ne ALLAH YA yiwa Galadiman Kano Yusufu rasuwa a garin Takai. To amma lokacin da ciwon ajali ya kama shi, sai ya rubuta wasiyya akan cewar, idan ya mutu, to a nada daya daga cikin kannen sa wato Alu.

To ance an gwabza yaki na karshe tsakanin rundunar Sarkin Kano Tukur da ta Yan tawaye a Tafashiya kusa da Tsanyawa, inda aka yi nasara akan Sarkin Kano Tukur har ma ya rasa ransa a 1893 bayan yayi yan watanni yana Sarkin Kano.

 

SARKIN KANO ALU MAISANGO (1893 – 1903)

Sarkin Kano Alu Maisango dan Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi dan Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo ya zama Sarkin Kano na bakwai a Tarihin Mulkin Fulani a Masarautar Kano a cikin shekarar 1893. Ya zama sarki ne bayan da aka gama rigimar Basasar Kano wadda ta kawo karshen mulkin Sarkin Kano Tukur.

Masana tarihin Kano sun bayyana Sarkin Kano Alu Maisango a matsayin sarki marar tsoro, kuma gwanin yaki.

 

An ce lokacin da Sarkin Kano Alu Maisango ya zama Sarkin Kano, ya tarar da cewa akwai alaka mai tsami tsakanin Kano da Damagaram. Don haka ya himmatu wajen ganin ya murkushe barazanar Damagaram, kuma ya saka ta tabi Kano dole. An ce an buga wani kazamin yaki tsakanin mayakan Kano bisa jagorancin Sarki Alu, da kuma na Damagaram bisa jagorancin Sarkin Damagaram Ahmadu a Gezawa ta Kasar Kano. A yakin, Sarkin Kano Alu Maisango ya nuna jarumtaka kwarai da gaske inda yayi wa babban mayakin nan na Damagaram wato Mayana kisan wulakanci ta hanyar raba shi gida biyu da takobi. Wannan dalili ne yasa da Sarkin Damagaram Ahmadu yaga kisan da aka yi wa Mayana, sai ya janye dakarun sa suka gudu, su kuma mayakan Kano suka bi su har bakin iyaka.

 

Zuwan Turawa Kano a 1903

Tarihi ya bayyana cewa, tun cikin shekarar 1900 Turawan Ingila (England) suka kafa mulkin su a Arewacin Nigeria, to amma sun kasa mamayar Kano da Sokoto. To ana cikin wannan yanayi ne, sai Magajin Garin Keffi Ibrahim Dan Yamusa ya kashe wani baturen soja mai suna Kyaftin Maloney, kuma sai ya gudo Kano inda Sarkin Kano Alu Maisango ya bashi mafaka. Wannan abu kuwa ya bakantawa Turawa rai, don haka ne suka shirya rundunar soji don su zo su murkushe Kano.

Tarihi ya tabbatar da cewa, Turawa sun iso Kano ne a ranar 2 ga Janairu, 1903. To amma sai aka samu akasi Sarkin Kano Alu Maisango ya tafi ziyara Sokoto. Ance sojin Turawan sun rabu zuwa Kofofin Kabuga, Dukawuya, da kuma Kofar Gadon Kaya, inda suka yi amfani da manyan bidigogin su wajen karya kyauren wadannan Kofofi. Daga nan, suka sami damar shiga cikin birnin Kano, su kuma Kanawa daga ganin sojin Turawa sai suka dinga gudu suna kiran “ga nasarana nan, kowa yayi ta kan sa”.

Tarihi ya tabbatar da cewa, a lokacin da sojin Turawa suka isa Gidan Sarkin Kano, sai da aka buga wani karamin yaki, inda Sallaman Kano Jatau da kuma Sarkin Shanun Kano Dangwari da wasu dakaru suka hana Turawa shiga Gidan Sarautar Kano. To amma da yake su Turawa sun fi Kanawa kayan fada masu kyau, ba’a dade ba suka murkushe wannan fito na fito. Kuma suka shiga Gidan Sarautar Kano, wanda ya tabbatar da cewa Kano ta kwanta dama.

A bangaren ziyarar Sarkin Kano Alu Maisango kuwa, bayan ya gama ziyarar ne ya taho, sai ya sami labarin cewa Turawa sun cinye Kano. Don haka ne bayan yayi shawara, sai ya sulale tare da wasu bayin sa cikin dare ya bar tawagar sa, inda ya yi nufin ya tafi Sudan domin yaje gurin dan gwagwarmayar nan da yake yakar Turawa wato Mehdi. To amma bayan yayi wasu kwanaki yana tafiya, sai Turawan Faransa suka kama shi, kuma suka mika shi ga Turawan Ingila, su kuma suka kai shi Lokoja suka ajiye shi har karshen rayuwar sa a 1926.

A bangaren tawagar da Sarkin Kano Alu Maisango yaje da ita Sokoto, bayan gari ya waye sai suka nemi Sarkin Kano basu ganshi ba. Don haka sai suka yi shawara akan ko su tafi Kano su yaki Turawa ko kuma suyi sulhu da Turawan. To ance wasu karkashin Wazirin Kano Ahmadu sai suka ce su ba za su yi sulhu da Turawa ba, hasali ma sai dai yaki tsakanin su. Sauran kuma karkashin Wamban Kano Abbas, sai suka yanke shawarar su dawo Kano suyi sulhu da Turawa.

Masana tarihin Kano sun ce, tawaga ta farko karkashin Wazirin Kano Ahmadu, bayan sun taho Kano ne, sai suka yi arangama da Turawa a Kwatarkwashi cikin kasar Zamfara. An kuma buga yaki, har dai Turawan suka sami nasarar kashe Wazirin Kano Ahmadu, wanda ita ta saka sauran dakaru suka bada kai ga Turawa.

Su kuma tawaga ta biyu, karkashin Wamban Kano Abbas, sai suka dawo Kano suka nemi sulhu da Turawa, kuma Turawan suka yarda, har ma Gwamnan Nigeria ta Arewa Lord Lugard ya nada Wamban Kano Abbas a matsayin sabon Sarkin.

 

SARKIN KANO ABBAS (1903 – 1919)

Hoton Sarkin Kano Abbas

Sarkin Kano Abbas dan Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi dan Sarkin Kano Ibrahim Dabo ya zama Sarkin Kano na takwas a Tarihin Mulkin Fulani a Masarautar Kano bayan da Turawan Ingila suka cinye Kano da kuma Daular Usmaniyya ta Sokoto baki daya cikin 1903.

Tarihi ya tabbatar da cewa shi Sarkin Kano Abbas ya kasance mutum ne mai hakuri, kyauta, da kuma tafiya da zamani. Wannan ce ma ta saka abubuwan zamani na farko suka samu sosai a zaminin sa kamar haka :

 • A zamanin na Sarkin Kano Abbas, Turawa a Kano karkashin Razdan din Kano (Residents ) wato Dr. Cargill an raba Kano zuwa gundumomi (districts), kuma aka nada hakimai (district heads) a kowace gunduma, a shekarar 1907
 • Haka kuma an bude makarantar boko ta farko a 1909, wanda gurbin ta a yanzu yake Gidan Danhausa (Kano State History & Culture Bureau)
 • Sannan hanyar jirgin kasa ta karaso Kano daga Lagos cikin 1912.

Wadannan sune muhimmai daga cikin ayyukan ci gaban zamani da suka faru a zamanin Sarkin Kano Abbas.

Sarkin Kano Abbas ya rasu ne a shekarar 1919 aka kuma binne shi a Gidan Sarki na Nassarawa, bayan ya kwashe shekaru 16 yana Sarkin Kano.

 

SARKIN KANO USMAN DANTSOHO (1919 – 1926)

Hoton Sarkin Kano Usman Dantsoho

Sarkin Kano Usman wanda ake wa lakabi da ‘Dantsoho’, dan Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi dan Sarkin Kano Ibrahim Dabo ya zama Sarkin Kano na tara a Tarhin Mulkin Fulani a Masarautar Kano a shekarar 1919, bayan rasuwar kanin sa Sarkin Kano Abbas.

A zamanin sarautar Sarkin Kano Usman Dantsoho, Turawan kasashen waje suka fara kafa kamfanoni a Kano, kamar su Kamfanin Neja (Niger Company), UAC, GBO, da kuma Gidan Goldie. Don haka ne ma sabbin yan Kasuwa suka kara bayyana ta hanyar yin hulda da wadannan Turawan Kamfani. Yan kasuwar kuwa sun hada da kamar su Alhaji Alhassan Dantata, Alhaji Nabegu, Alhaji Danbaffa, da kuma sauran su.

Haka kuma a zamanin Sarkin Kano Usman Dantsoho ne, dan Sarkin Ingila Prince Edward ya ziyarci Kano a 1925. Kuma yazo ne a jirgin sama, wanda ya bawa Kano damar zama gari na farko da jirgin sama ya fara sauka a Nigeria.

Sarkin Kano Usman Dantsoho ya rasu ranar 23 ga May, 1926.

 

SARKIN KANO ABDULLAHI BAYERO (1926 – 1953)

 

Sarkin Kano Abdullahi Bayero dan Sarkin Kano Abbas dan Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi dan Sarkin Kano Ibrahim Dabo, ya zama Sarkin Kano na goma a Tarihin Mulkin Fulani a Masarautar Kano a shekarar 1926, bayan kawun sa Sarkin Kano Usman Dantsoho ya rasu.

Masana tarihin Kano sun bayyana Sarkin Kano Abdullahi Bayero da cewa mutum ne mai kwarjini da kuma kasaitar sarauta. Don haka ne ma yake kokarin tafiya da zamani a duk al’amuran sa. Kuma wannan ita ce ta saka ya zama Sarkin Kano na farko da ya fara fita zuwa kasar waje, inda da farko yaje Ingila a 1934, sannan ya zama Sarkin da ya fara zuwa aikin Hajji, wanda yaje a cikin shekarar 1936.

Zamanin Sarkin Kano Abdullahi Bayero ne ci gaban zamani na ainihi ya fara zuwa Kano. Da farko an gina Makarantar Midil (Rumfa College) a 1927, sannan kuma a 1928 aka kawo wutar lantarki da ruwan famfo.

Taswirar Masarautar Kano mai nuna gundumomin hakimai a shekarar 1950
Taswirar birnin Kano a shekarar 1950

Sarkin Kano Abdullahi Bayero ya rasu a ranar 23 ga Disamba, 1953. Bayan ya kwashe shekaru 27 yana sarautar Kano.

 

 

 

 

Sarkin Kano Abdullahi Bayero lokacin da ya dawo daga wata tafiya a motar sa

 

SARKIN KANO Sir MUHAMMADU SANUSI I (1954 – 1963)

Hoton Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I dan Sarkin Kano Abdullahi Bayero dan Sarkin Kano Abbas dan Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi dan Sarkin Ibrahim Dabo, ya zama Sarkin Kano ne a cikin shekarar 1954, bayan rasuwar mahaifin sa Sarkin Kano Abdullahi Bayero.

Masana tarihin Kano sun bayyana Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I da cewa Sarki ne mai kwarjini, rashin tsoro, da kuma rashin daukar raini. Sannan kuma mutum ne mai ilmin Addinin Musulunci mai zurfi. Har ance lokacin yana Sarkin Kano, duk Sarakunan Nigeria ta Arewa sun kasance suna bashi girma na musamman. Wannan dalili ne ma yasa ya taba zama Mukaddashin Gwamnan Jihar Arewa na wani dan lokaci.

A zamanin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I, Sarauniyar Ingila Elizabeth II ta ziyarci Kano cikin shekarar 1956, inda Sarkin ya shirya mata hawan dawakai na alfarma wato a turance durbar, sannan kuma aka zagaya da ita cikin Gidan Sarautar Kano. Kuma Sarauniyar Ingila Elizabeth II ta bashi lambar girmamawa ta KMG wato ‘Sir”.

 

Sarkin Kano Sir Muhammadu Sanusi I tare da bakuwar sa Sarauniyar Ingila Elizabeth II da kuma mijin ta Prince Philip, daga gefe kuma Alhaji Yusuf Maitama Sule yana yi musu bayani a cikin shekarar 1956

 

Sarkin Kano Sir Muhammadu Sanusi I yayi murabus daga matsayin Sarkin Kano, bayan da Kwamitin Muffett ya binciki yadda NA ta Kano (Native Authority) take kashe kudadenta.

 

SARKIN KANO MUHAMMADU INUWA (1963 – 1963 wata 7 kawai yayi)

Hoton Sarkin Kano Muhammadu Inuwa

Sarkin Kano Muhammadu Inuwa dan Sarkin Kano Abbas dan Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi dan Sarkin Kano Ibrahim Dabo, ya zama Sarkin Kano a 1963 bayan da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I yayi murabus.

Masana tarihi a Kano sun bayyana Sarkin Kano Muhammadu Inuwa a matsayin mutum mai hakuri da juriya a mu’amular sa da jama’a.

Sarkin Kano Muhammadu Inuwa ya rasu a shekarar 1963, bayan dan gajeren lokaci na watanni 7 a gadon Sarautar Kano.

 

SARKIN KANO ADO BAYERO (1963 – 2014)

 

Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero rike da Tagwayen Masu

Sarkin Kano Ado dan Sarkin Kano Abdullahi Bayero dan Sarkin Kano Abbas dan Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi dan Sarkin Kano Ibrahim Dabo, ya zama Sarkin Kano ne bayan rasuwar Kawun sa wato Sarkin Kano Muhammadu Inuwa a shekarar 1963. Shine Sarki na 13 a jerin Sarakunan Kano Fulani, kuma na 56 a jerin Sarakunan Kano baki daya.

Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero kamar yadda mafi yawancin mutane suka san shi, mutum ne mai kwarjini fiye da duk sauran Sarakunan Kano da aka yi. Wannan dalili ne yasa ya samu shahara da kuma alfarma a gurare da dama a duniya. Sannan shi Sarkin Kano Ado Bayero, shine Sarki na farko a Kano mai tsantsar ilmin boko, don haka ya taka rawar gani a tarihin Nigeria musamman a lokacin Juyin Mulkin Nigeria na farko da kuma Yakin Basasar Nigeria.

A bangaren alakar sa da sauran manyan mutane a duniya, ya kasance wasu shugabannin kasashe da kuma manyan jami’an huldar diflomasiyya duk sun halarci fadar sa a lokutai daban daban. Wadannan mutane sun hada da dan Sarauniyar Ingila Elizabeth II wato Prince Charles, Shugaban Habasha (Ethiopia) Haile Selassie, Shugaban Tanzania Julius Nyerere, Shugaban Zimbabwe Robert Mogabe, Shugaban Ghana Jerry Rawlings, Shugaban Libya Mu’ammar Ghaddafi, da sauran su.

 

Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero yana jawabi lokacin yayin da Shugaban Nigeria Ibrahim Babangida da kuma babban bako Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe suke sauraro a Fadar Kano a cikin shekarar 1990
Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero tare da Sakatariyar Wajen Amurka wato Madeline Albright a Fadar Kano.

Wadannan hotunan da suke sama, suna nuna wasu daga cikin ziyarori da Manyan Mutane suka kawo wa Maimartaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero.

Sarkin Kano Ado Bayero a Lokacin da Kano ta zama Jiha.

Kafin Kano ta zama Jiha a 1967, Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero shine mafi iko wajen tafiyar da mulkin Lardin Kano, wato shine Shugaban N.A. (Native Authority). To amma sakamakon kirkiro Jihohi da Shugaban Nigeria Yakubu Gowon yayi da kuma kawo Tsarin Kananan Hukumomi da Shugaban Nigeria Murtala Muhammad yayi, sai ya zamana Sarkin Kano dama sauran Sarakuna, sun rasa ikon su na gudanarwa wato a turance ‘Executive Role, zuwa kawai matsayin Iyayen Kasa wato a turance ‘Ceremonial Role’. Don haka Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero yayi zamani da Gwamnonin Soja da na Farar Hula guda 14 kamar haka :

 1. Audu Bako (1967 – 1975)
 2. Colonel Sani Bello (1975 – 1978)
 3. Group Captain Ishaya Shekari (1978 – 1979)
 4. Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi (1979 – 1983)
 5. Alhaji Audu Dawakin Tofa (1983 – 1983)
 6. Alhaji Sabo Bakin Zuwo (October 1983 – December 1983)
 7. Air Commodore Hamza Abdullahi (1984 – 1985)
 8. Colonel Ahmad Daku (1985 – 1986)
 9. Air Commodore Ndatsu Umaru (1986 – 1988)
 10. Colonel Idris Garba (1988 – 1991)
 11. Architect Kabiru Gaya (1991 – 1993)
 12. Colonel Muhammad Abdullahi Wase (1993 – 1996)
 13. Colonel Dominic Oneya (1996 – 1998)
 14. Colonel Aminu Isa Kontagora (1998 – 199)
 15. Engineer Rabiu Musa Kwankwaso (1999 – 2003)
 16. Malam Ibrahim Shekarau (2003 – 2011)
 17. Engineer Rabiu Musa Kwankwaso (2011 – 2015)

Raba Jihar Kano gida biyu

A zamanin Maimartaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ne, a shekarar 1991 Gwamnatin Nigeria karkashin General Ibrahim Babangida ta raba Jihar Kano, inda aka kirkiro Jihar Jigawa. Saboda haka wannan dalili yasa Masarautar Kano ta rasa wasu daga cikin Gundumomin Hakimai da suka hada da Dutse, Birnin Kudu, Gwaram, Ringim, Jahun, Kiyawa, Taura, Garki, da kuma Babura.

Taswirar Gundumomin Hakimai a Masarautar Kano zuwa shekarar 1990

 

Da yake Shi Maimartaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya zama Sarkin Kano ne a zamanin da Nigeria bata dade da samun yancin kai ba, wannan ya bashi samun damar damawa a cikin abubuwa da dama a Nigeria. Wadannan abubuwa sun hada da kamar :

Rasuwar Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero

Maimartaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya rasu a ranar 6 ga June, 2014, yana dan shekara 84, kuma bayan ya kwashe shekaru 51 yana sarautar Kano.

 

SARKIN KANO MUHAMMADU SANUSI II (2014 – HAR ZUWA YAU)

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II dan Ciroman Kano Aminu dan Sarkin Kano Sir Muhammadu Sanusi I dan Sarkin Kano Abdullahi Bayero dan Sarkin Kano Abbas dan Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi dan Sarkin Kano Ibrahim Dabo, ya zama Sarkin Kano ne bayan rasuwar Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero a shekarar 2014.

Sarkin Kano Sanusi II ya kasance mai ilmin boko dana Addinin mai zurfi. Wannan ta saka ya rike mukamin Gwamnan Babban Bankin Nigeria a tsakanin shekarar 2009 zuwa 2014 kafin ya zama Sarkin Kano. Kuma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya kasance mutum marar tsoro dan gwagwarmaya, kuma mai fadar gaskiya a duk lokacin da ya dace. Wannan kuma ya bashi damar samun matsayin mutum wanda a duk fadin Nigeria aka san shi wajen bada shawarwari akan yadda za’a gyara tattalin arzikin kasa.

 

Wasu daga Cikin Hotunan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a cikin Shigar Sunkumai a ranar Sallar Idi

 

 

KAMMALAWA

Kamar yadda muka kawo bayani daban daban akan Kafuwar Masarautar Kano tun daga Jihadi 1807 zuwa yau, zamu ga cewa Masarautar Kano ta shiga yanayi daban daban wanda ya hada da yake-yaken tawaye a zamanin Sarkin Kano Ibrahim Dabo, Basasar Kano ta shekarar 1893, zuwan Turawan Ingila Kano a 1903, ci gaban zamani a lokacin Turawa, da kuma kasantuwar Masarautar Kano bayan samun Yancin Kan Nigeria a 1960 da kuma karbe iko daga hannun Sarakunan Gargajiya daga baya.

A takaice Masarautar Kano karkashin ikon Fulani ta shiga yanayin chanji daban-daban tun daga 1807 zuwa yau, wato kimanin shekaru 212 kenan.

 

 

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

3 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button